23 Nuwamba 2020 - 17:49
Kafafen Isra’ila: Netanyahu Ya Gana Da Bin Salman Da Pompeo A Asirce A Saudiyya

Kafafen watsa labaran Isra’ila sun bayyana cewar firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ilan Benjamin Netanyahu ya tafi kasar Saudiyya jiya Lahadi a asirce don ganawa da yarima mai jiran gado na Saudiyyan Mohammad Bin Salman da kuma Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ke ziyara a can.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce gidan radion Kan da kuma radion sojojin Isra’ilan ne suka ba da wannan labarin inda suka ce a jiya Lahadi ne Firayi minista Netanyahun wanda ya ke samun rakiyar shugaban kungiyar leken asirin Isra’ilan (MOSSAD) Yossi Cohen wanda ke jagorantar kokarin da ake yi na kulla alaka tsakanin Isra’ila da kasashen larabawa.

Har ya zuwa yanzu dai ofishin Netanyahun da kuma ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Kudus bugu da kari kan mahukuntan Saudiyyan ba su ce komai kan wannan labarin wajen tabbatarwa ko kuma kore shi ba.

Wasu kafafen watsa labaran Isra’ilan sun ce an gudanar da ganawar ce a garin Neom, wani sabon garin da Saudiyya take ginawa.

Wannan ganawar dai tana zuwa a daidai lokacin da a ‘yan kwanakin da suka gabata sakataren wajen Amurkan Mike Pompeo ya sanar da cewa yana da kwarin gwiwan cewa akwai wasu kasashen larabawa da za su shigo sahun kasashen da suka kulla alaka da Isra’ilan, sannan kuma a shekaran jiya ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan ya sanar da cewa Saudiyyan na goyon bayan kulla cikakkiyar alaka da Isra’ilan idan har za a cika wasu sharudda.

Har ya zuwa yanzu dai Saudiyyan ta ki amincewa da kulla alaka da Isra’ila, to sai dai tun daga watan Augustan da ya gabata ta fara barin jiragen saman Isra’ila suna wucewa ta sararin samaniyyarta zuwa wasu kasashen Tekun Fasha da sauransu lamarin da ake ganinsa a matsayin mafarin kulla wannan alakar.

Wasu rahotanni sun ce shugaban kasar Amurka Donald Trump yana ta matsin lamba wa kasar Saudiyyan wajen ta shigo sahun kasashen larabawan da suka kulla alaka da Isra’ila da suka hada da UAE, Bahrain da kuma Sudan, wanda ake ganin wannan ita ce ma manufar ziyara da Mike Pompeo yake yi a yankin Gabas ta tsakiyan a halin yanzu.

342/